29/09/2026
Wani mutumin Turkiya da ya shaida faruwar wani babban al'amari da idonsa a masallacin Annabi (ﷺ) ya ba da labari ya ce:
Ina tsaye a masallacin Manzon Allah (ﷺ) sai na ga wasu ƴansanda suna jiran wani mutum ya fito, can sai ga wani matashi ya fito daga masallacin, nan take s**a k**a shi s**a saka masa ankwa.
Wannan matashi ya ce musu cikin sanyin murya: “ku barni na yi sallah na yi addu'a, ni ba mabaraci ba ne, kuma ba ɓarawo ba ne...”
Mai ba da labarin ya ce, sai na ga k**ar na waye shi, saboda na lura da cewa, ina yawan ganinsa a masallacin Annabi (ﷺ) kowane lokaci, mutumin ƙasar Albaniya ne wanda shekarunsa suke tsakanin 35-36 a duniya.
Sai na tambayi ƴansandan, “shin wane laifi ya yi haka?” Sai s**a ce, “yana zaune a Madina ne tsawon shekaru shida ba bisa ƙa'ida ba, shi ne muke so mu mai da shi ƙasarsu, amma yana ta ci gaba da guje mana yana fakewa a masallacin Annabi (ﷺ)”
A gefe guda, amma shi wannan matashi yana ta ci gaba da kuka yana cewa, “mene ne zai faru don kun kyale ni na tafi kaya na?! Ni ba ɓarawo ba ne, kuma bana roƙo anan, ina Madina ne saboda soyayyar Annabi (ﷺ) ku ƙyale ni...” 😭
Ƴan sandan s**a ce: “ba fa za mu ƙyale ka ka ci gaba da zama anan ba,” matashin ya roƙe su su barshi ya yi addu'a da sallama ga Annabi (ﷺ), sai ƴansandan s**a amince s**a ƙyale shi.
Sai ya ɗaga murya yana kuka yana cewa: “Ya Manzon Allah! Yanzu shin ba na bar iyaye na ba ne, na kulle kasuwancina na bar komai nawa don na zo nan na zauna kusa da kai ba?! 😭 Ya Rasulullah!
Can kawai sai aka ga wannan bawon Allah matashi ya yanki jiki ya faɗi ƙasa warwas bai cikin hayyacinsa, da farko ƴansanda sun tsammaci yana pretending ne kawai, da s**a duba sai s**a ga ashe tuni Allah ya ƙarɓi rayuwarsa yana cikin wannan munajati da Manzon Allah (ﷺ).
Nan fa ƴansanda jikinsu ya yi sanyi, s**a fara nadama suna cewa, “wai me yasa ba mu gane cewa yana son manzon Allah (ﷺ) haka ba?!
Mai bada labarin ya ce: ina tsaye a wajen aka ɗauke shi don a masa sutura a masa sallah, su kuwa wa