04/02/2026
Yan Najeriya a Yaƙin Ukraine da Russia – Abin da Ya Kamata Mutanenmu Su Sani
Gaskiya, duk wanda ya yanke shawarar zuwa aikin soja, ya riga ya san abin da ke gaba. Ni kaina a watan Nuwamba, akwai wadanda s**a sanar da ni cewa idan muka je, za a rika biyan mu $2,600 a duk wata bayan horon sati uku, sannan daga ranar da muka isa za a fara ba mu allowances a matsayin sojojin sa-kai. Amma k**ar yadda rayuwa take, ba komai ne yake tafiya da alkawari ba.
Yaƙin da ke gudana tsakanin Ukraine da Russia ya zama ɗaya daga cikin yaƙe-yaƙe mafi tsanani tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu. Dalili kuwa shi ne, bangarorin biyu sun shiga da cikakken shiri—duk abin da suke da shi suna amfani da shi domin samun nasara.
Ukraine na samun cikakken goyon baya daga kasashen Turai da Amurka, yayin da Rasha ita ma ke daga cikin manyan ƙasashe masu ƙarfi a fannin soja, tare da taimakon mak**ai daga ƙasashe irin su Korea ta Arewa da Iran.
Yanzu haka, yaƙin ya shiga shekara ta huɗu, kuma babu wata alamar tsagaita wuta, duk da yunƙurin da aka yi na sasanci tsakanin Zelensky da Putin, ciki har da ƙoƙarin da Trump ya taɓa yi.
Tun farkon yaƙin, ana ɗaukar sojojin haya ta hanyoyi daban-daban. Rasha ta fi mayar da hankali wajen ɗaukar matasa daga ƙasashen Larabawa da Musulmi, musamman waɗanda ke fama da rikice-rikice k**ar Yemen, Syria, Iraq, Afghanistan da mak**antansu.
A ɓangaren Ukraine kuwa, suna samun sojojin sa-kai daga kasashen Turai da Amurka—akwai daga Birtaniya, Amurka, Jamus, Faransa da sauransu.
Daga baya kuma, Rasha ta fara karkata zuwa nahiyar Africa, inda ake yaudarar matasa da alkawarin ayyuka k**ar na masana’antu ko tuƙi, albashi mai yawa, ko ma takardar zama ɗan ƙasa. Amma gaskiya ita ce, da zarar mutum ya isa, yana iya tsintar kansa a filin daga.
Hasashen da yawa na nuna cewa damar tsira ƙanana ce sosai—ko dai mutum ya mutu, ko a k**a shi a matsayin fursunan yaƙi. Idan kuma aka ɗauke shi sojan yaƙi kai tsaye, akwai yiwuwar a gurfanar da shi a kotun soji. Abin takaici, galibin waɗannan ma