Ahlulbaiti Mohammad S.A.W

Ahlulbaiti Mohammad S.A.W FITO DA DARAJA DA KIMAR GIDAN ANNABI MUHAMMAD S.A.W

20/10/2021

Fitacciyar jarumar fina -finai a cikin shirin DadinKowa na gidan talabijin na Arewa24, Sarah Aloysius, ta ce matuƙar girmamawar da take yi wa Annabin Musulunci, Muhammad (S. A. W) ne ta sa aka ganta tana rera wakokin yabonsa cikin harshen Larabci a wani faifan bidiyo a shafukanta na Sada Zumunta. J...

16/10/2020

Ga kadan daga cikin Sunayen maulaty sayyida Nana fadimatuz-zahra'u(as)*
1 *_Abida_*
2 *Aliema*
3 *Arradiyya*
4 *Alawiyya*
5 *Atika*
6 *Azeema*
7 *Azeeza*
8 *Amira*
9 *Aliyya*
10 *Batula*
11 *Baki'a*
12 *Baraka*
13 *Bintul rasul*
14 *Bidi'atu mustapha*
15 *Dayyiba*
16 *Dahira*
17 *Fatima*
18 *Farida*
19 *Fa'ika*
20 *Fa'iza*
21 *Fauziyya*
22 *Fadila*
23 *Fasiha*
24 *Husna*
25 *Hafiza*
26 *Halima*
27 *Hani'a*
28 *Hamida*
29 *Harira*
30 *Hakima*
31 *Hauraul insiyya*
33 *Iklima*
34 *Jamila*
35 *Kausara*
36 *Kuratu ainul rasul*
37 *Khairiyya*
38 *Latifa*
39 *Munira*
40 *Muhaddasa*
41 *Mardiyya*
42 *Makiya*
43 *Madaniyya*
44 *Mazluma*
45 *Mu'umina*
46 *Mubaraka*
47 *Muddahara*
48 *Mukarrima*
49 *Maimuna*
50 *Ma'arufa*
51 *Mashkura*
52 *Muhsina*
53 *Mansura*
54 *Mujahida*
55 *Magsuba*
56 *Makhoura*
57 *Mubashshira*
58 *Nuriyya*
59 *Nabawiyya*
60 *Nakiya*
61 *Nabila*
62 *Najma*
63 *Na'ima*
64 *Nafisa*
65 *Qamariyya*
66 *Qayyuma*
67 *Radiya*
68 *Rahima*
69 *Ra'ufa*
70 *Rafi'a*
71 *Rahina*
72 *Rashida*
73 *Sajida*
74 *Siddika*
75 *Sabira*
76 *Shahida*
77 *Shafi'a*
78 *Sharifa*
79 *Safina*
80 *Salima*
81 *Saliha*
82 *Safwa*
83 *Sayyidatul nisa'il alamin*
84 *Tuhfatul fiddausi*
85 *Takiyya*
86 *Ummul khairi*
87 *Ummul Azhar*
88 *Ummu Abiha*
89 *Ummu aimana*
90 *Wasila*
91 *Walida*
92 *yasira*
93 *Zakiyya*
94 *Zahida*
95 *Zakira*
96 *zuhuriyya*
97 *zahara*
98 *Zunnura*
99* zam-zamiya
100* zaliha

Dan kaunarka/ki da Nana fadima as. Ku turawa yan masoya sayyada as... Suma su amfana👏

19/01/2020

*TUNATARWAR DARE*
*YANDA AKE AMBATON ALLAH*

204.Kuma idan an karanta Alƙur'ãni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammãninku, anã yi muku rahama.

205.Kuma ka ambaci Ubangijinka, a cikin ranka da ƙanƙan da kai, da tsõro, kuma kõmabãyan bayyanawa na magana, da sãfe da marece, kuma kada ka kasance daga gafalallu.

*SURATUL A'ARAF*

18/11/2019

MAULUD MAULUD MAULUD Malam Nura Na Mal. Garba Mai Tafsir (R.A).
Yana Gayyatarka/ki Taron Maulidin MANZON ALLAH (S.A.W). Tare Da Daurin Auren Kannansa Su Shida (6).
RANA: Asabar 23-Nov-2019.
LOKACI: 7:00am zuwa 10:00am (na safe).
WURI: Kofar Gidansa, Sabon Gari Gashua, Jahar Yobe.

17/11/2019
17/11/2019

Labbaika Ya Rasulillahi

28/12/2018

-Kayi riko da imani da kokarin neman ilimin addini da yawan ibada hakan zai sa ka rayu cikin yardar Allah.

-Kafin kayi rubutu kayi nazari akai, kuma kafin kayi magana kayi tunani akai, yin tunanin zai raba ka da yin abin dana sani a rayuwa..

-Duk abin da ya faru da kai kafin ka yanke hukunci kayi bincike akai, kuma duk abinda ya faru kayi hakuri da tawakkali, duk halin da ka samu kanka a ciki ka dogaro ga Allah.

-Ka natsu sosai yayin mu'amala da mutane, ka saurari mai zuwa maka da magana, ka sani ba ko wacce magana ake yarda da ita ba. Don ba kowane mai baka shawara ne ke nufin ka da alheri ba...

In an kawo maka labari kada kayi farat ka musanta, kayi sauraro: alamar cikar hankali ne. Tabbas ba kowacce magana ake karyatawa ba, zai yiwu ka samu mafita cikin maganar da ake kawo maka...

-Ka kame harshen ka daga kushe mutane, kullum ka zamo cikin masu fadin alheri akan mutane, Musulmi na kwarai yana kiyaye umarnin: "Fadi Alkairi ko kayi shiru"...

-Yi nazari ka dubi rayuwar ka da kyau, abin fata shine Ka yawaita aikata Alkairi fiye da Sharri, haka nan kafi yawaita fadin gaskiya...

- Ka nisanci hassada da aibata mutane, Ka yawaita kyakyawar addu'a da fata akan ka da mutane fiye da mummuna...

-Kana yiwa mutane zaton alheri, kayi hakuri ka zauna da kowa da halin sa, ka sani ba kowa bane mutumin kirki, hakanan ba kowa bane mutumin banza..

-Ka nisanci mummunar dabi'ar yawan zagi, tabbas yawan ashar da zage-zage alama ce ta ashararanci da rashin nagarta. Ka rike mutuncinka kar kana zagin kowa, kuma in an zage ka kayi hakuri ka yafe, ka sani zagin zai koma kan wanda ya zage ka.

- Ka zamo mai godiya da yabawa wanda duk yayi maka alheri komi nisan lokaci. Hakika manta alheri da butulcewa mutane shukawa kai sharri ne kuma aikin marasa imaani ne...

-Ka kyautata zato ga Allah, kuma kafin ka roki wani abu gun Allah ka yi masa godiya akan abinda kake dashi, ka sani rai da lafiya ma arziki ne. Yawan korafi da koke-koke alamar rashin godiya ne da butulci ga Allah...

- Ka s

Address

Gashua

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ahlulbaiti Mohammad S.A.W posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The University

Send a message to Ahlulbaiti Mohammad S.A.W:

Share