Jibwis Nigeria. Jingir Bassa L G C Branch.

Jibwis Nigeria. Jingir Bassa L G C Branch. Masjidu al-kitabu wassunnah Jengre

SADAKA MAI GUDANA, ASSALLAMU ALAIKUM YAN UWA MUSSULMI, KOMITIN MASALACIN JUMA A, NA MASJID ALKITABU WASSUNNA JINGIR NA N...
14/11/2022

SADAKA MAI GUDANA, ASSALLAMU ALAIKUM YAN UWA MUSSULMI, KOMITIN MASALACIN JUMA A, NA MASJID ALKITABU WASSUNNA JINGIR NA NEMAN TAIMAKONKU DON SAYAN GURIN DA ZA A GINA BABAN MASALLACIN JUMA A DON HAKA MU HADA HANNU WAJEN WANNAN AIKIN TA TURA SADAKARKU KOMAI KARANCINSA TA WANNAN ACCOUNT, (JAIZ BANK ,0006201663, MU AZU BALA), ALLAH YA BADA IKON TAIMAKAWA DON KARIN BAYANI SAI AKIRA 08069541354 SAKATARE KO 07036898969 SHUGABAN AGAJI KO 08065807850 CIYAMAN,

05/11/2022

DUK LAIFIN DA DAN ADAM YAKE AIKATAWA YASANI, HAKAMA ALKAIRI YA SANI, TO MUNADA SAURAN LOKACIN TUBA.

04/11/2022

YA ALLAH, KASA WANNAN SALLAR JUMA'A, TA ZAMA KARBABIYA GA DUKKAN MUSSULMI AMIN.

07/09/2022
26/08/2022
24/08/2022

Kungiyar IZALA ta tara kudi Naira miliyan dari da bakwai ta dalilin tattara fatun layya (₦107,704,484.25)

✍️Ibrahim Baba Suleiman

Kungiyar wa'azin musulunci mai kira a kau da bidi'a a tsaida sunnar Annabi Muhammad mai tsira da aminci, ta tara naira miliyan dari da bakwai da dari bakwai da hudu da naira dari hudu da hudu da kwabo ashirin da biyar (₦107,704,484.25) na tattara fatun layyan da ya gabata na shekarar 1443/2022.

A bana Jihar da tafi ko wace jiha kawo kudi itace jihar Sokoto inda ta tara Naira miliyan goma sha uku da dubu dari takwas da tamanin da shida da naira hamsin kacal (13,886,050,00)

Jihar kaduna ita tayi na biyu inda ta tara fatun Naira miliyan goma sha uku da dubu dari uku da talatin da tara da naira dari shida kacal. (₦13,339,600.00).

Jihar Kebbi ita tayi na uku inda ta tara fatun Naira miliyan goma da dubu dari da sha biyar da naira dari biyu da tamanin kacal. (₦10,115,280,00)

Haka lamarin ya gudana a dukkan jihohin Naijeria talatin da shida harda Abuja.

A cikin bayanan sa shugaban IZALA na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yabawa al'ummar kasar matuka wajen bada hadin kai a wannan aikin tare da tabbatar da gudanar da kudaden kamar yadda yakamata, ya kuma yabawa tare da jinjina ga kwamitin tattara fatun layyan da kwamandojin agaji da s**a tura wakilai a ko wace jiha kuma s**a jajirce wajen ganin aikin ya gudana yadda ake bukata.

A baya angina katafaren masallaci da gidan shan magani gami da katafaren masaukin baki a cikin birnin Abuja duka da kudaden fatun layyan da jama'a ke badawa.

Allah ya sakawa duk wanda ya sanya jarinsa a wannan aiki da gidan Aljanna. Amin

JIBWIS NIGERIA 🇳🇬
[email protected]
25-Muharram-1444H
23-August--2022

08/08/2022

Tunatarwa:
Yau ita ce ranar Àshúra. Ranar da Manzon Allah (S) yake raya ta da azumi saboda murna kan Allah ya kubutar da dan uwansa Annabi Musa (AS), ya halaka Fir'auna.

Duk abinda aka yi a wannan rana in ban da azumi bidi'a ne.
Yan Shi'a suna makoki, jahilai suna cika-ciki.

Hadisan cika-ciki hadisan karya ne kuma sun ci karo da Hadisan azumi ingantattu. Amma saboda rashin sani a kasar Hausa sai a hada su gaba daya. A yini da azumi, ayi cika-ciki da daddare😁

Allah ya bar mu a kan tafarkin Manzonsa (S).

Rubutawar farfesa Mansur sokoto

🌿 🌷 🌿

Address

'Yan Haya Maiwada Street Jingir Jos
Jos

Telephone

+2348069541354

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis Nigeria. Jingir Bassa L G C Branch. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The University

Send a message to Jibwis Nigeria. Jingir Bassa L G C Branch.:

Share