31/07/2023
Motar Dangote ta Afka ga wani gida ta halaka mutum 3 suna kwance a daki a Zariya.
Daga Mahadi Hussaini Mediya Zariya.
“Motar dakon kaya na rukunin Kamfanin Dangote ta yi sanadiyar halaka mutum 3 a birnin Zariya jihar Kaduna.
Da safiyar yau litini Jaridar ALFIJIR HAUSA ke samun tabbacin faruwar Lamarin, inda mutum uku rigis s**a rigaye mu gidan gaskiya a sak**akon afka masu da motar dakon kaya na Dangote ta yi har cikin ɗaki.
Lamarin ya faru ne a daren jiya Lahadi cikin wani Anguwa da ake kira da anguwar juma dake birnin Zariya.
Wanda abin ya faru a idonsa ya ci gaba da shaidawa jaridar ALFIJIR HAUSA cewa, motar ta ƙwacewa direbanne a bayan haka sai ta Afka ga wannan gida, “inda ta halaka mutum 3 suna kwance a cikin ɗakinsu.”
Al'ummar anguwar sun matuƙan nuna alhininsu tare da kaɗuwa na faruwar wannan lamari, na rasa mutum 3 rigis a Loakci ɗaya.