14/09/2025
Failal Ahmadiy Feel Mauludin-Nabiyyi ❤️ Sallallahu Alaihi Wasallam ❤️
FAILAL AHMADIY (19)
Feel Mauludin-Nabiyyi ❤️ Sallallahu Alaihi Wasallam ❤️
WATA TARA DA DAUKAR CIKINSA DA ABUBUWAN MAMAKIN DA S**A BAYYANA GA SHUGABA AMINATU
1=Adare nafarko ga wannan wata farin ciki da murna s**a hadu ga Aminatu.
2=Adare na biyu akai mata Al-bishir da samun dukan abin burinta.
3=Adare na uku sai taji ana cewa da ita,Aminatu hakika kin dauki ciki da Wanda zai tashi da godiyar mu da yabonmu.
4=Adare na hudu sai tarika jin tasbihi na mala,iku Asama.
5=Adare na biyar taga Annabi Ibrahim abacci yana cewa da ita
Ina miki Al-bishir ya Aminatu da samun wannan Annabi madaukaki ma,abocin daraja da Alqadari.
6=Adare na shida farin ciki ya hadu ga Aminatu wannan farin ciki bai yanke mataba kuma bai raguba.
7=Adare na bakwai hasken yarda yadaukaka gareta inda yahada wadatuwarta.
8=Adare na takwas sai taji harshan murna da farin ciki suna kira suna cewa:-
Ya Aminatu haihuwar hasken-haske da watan watanni yayi kusa.
9=Adare na tara arzikinta da wadatarta sun bayyana agareta.
10=Adare na goma sai mala,iku s**a rude da tasbihi da godiya da yabo ga Ubangiji.
11=Adare na shadaya kasala da juyayi s**a gushe ga Aminatu.
12=Adare na shabiyu Shugaba Aminatu sai taji cewa abinda ke cikinta yanaso ya sauka tare da jin nakuda da alamarta.
Allahumma Salli, ala Sayyadi na Muhammadu Alfatihi Lima Ugliqa Walkhatimi Lima Sabaqa Nasirul-hakki Bil-hakki Walhadee ila Sirad'ukal Mustaqeemi Wa,ala alihi Haqqa qadarihee wa Miqidarihi-Azeem.