24/01/2026
BAYAN MALLAKAR PROFILE CODES - MENENE MATAKI NA GABA ?
• Sayen lambobin ePIN: shi ne mataki na gaba da ya kamata ɗalibi ya taka, bayan mallakar Profile Codes.
ePIN: lambobine guda 16 da ɗalibi yake saya, a madadin kuɗin rijistar jarrabawar JAMB baki ɗaya (ma'ana ba a bayar da kuɗi ga hukumar JAMB kaitsaye, waɗannan lambobin sune a madadin kuɗin).
YAUSHE AKE SAYEN ePIN ?
Tuni aka fara sayar da lambobin ePIN na jarrabawar JAMB ɗin shekarar 2026, kuma za a rufe sayar da lambobin ne kwanaki 2 kafin rufe rijistar JAMB ɗin baki ɗaya.
Babban abin farinciki game da mallakar JAMB PIN shi ne: Idan ɗalibi ya saya, Toh ya samu Security a wurin JAMB, domin har ƙarin kwanaki hukumar take yi wa waɗanda s**a mallaki PIN bayan an rufe.
A INA ZAMU IYA MALLAKAR PIN ?
Za ku iya mallakar lambobin ePINs ɗinku tun daga gida, kafin halartar CBT Centre, ta hanyar tuntuɓar Accredited PIN Vending Agent Mafi Kusa daku.
Sule Lamido University Kafin Hausa Connect