22/08/2026
ZIYARAR DAURIN AURE A GARIN DUNDU
A yau mun kai ziyara tare da girmamawa zuwa Daurin Auren da aka gudanar a Garin Dundu, inda Mai Girma Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar NDC Kwankwasiyya, Comr Aminu Abdussalam Gwarzo , ya halarta tare da Dan Takarar Majalissar Tarayya na Rano, Kibiya da Bunkure, Hon. Dr. Yusuf Jibril JY da kuma Dan takarar Sanata na Kano ta Kudu Hon. Nasiru Sule Garo
Wannan ziyara ta hada manyan jiga-jigan tafiyar NDC Kwankwasiyya, ciki har da Tsohon Kwamishina Hon. Aliyu Adamu Kibiya (DG Campaign), Hon. Jamilu Hassan Barrister (Secretary General Campaign), Hon. Bello Liman (Religious Affairs Campaign), da kuma Hon. Bilya Ahmad Rurum, tare da sauran masu ruwa da tsaki.
Ziyarar ta kasance wata dama ta nuna goyon baya, zumunci da girmama al’ummar Garin Dundu, tare da taya iyalan ango da amarya murnar wannan babban lokaci.
Bayan haka an karbi jagororin jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar NDC Kwankwasiyya.
Muna addu’ar Allah Ya sanya albarka a cikin wannan aure, Ya ba ma’auratan zaman lafiya, soyayya da fahimtar juna, Ya kuma albarkaci zuriyarsu. 🤲
BANGAJIYA TA MUSAMMAN!
Allah Ya kara hada kan al’ummar Rano, Kibiya da Bunkure, Ya kuma tabbatar da alheri a tafiyar NDC Kwankwasiyya.
_ Nazeer Sanata
~ JY MEDIA TEAM