07/06/2023
DUKKAN MU NAN MATAFIYA NE.
Kowa akan layin tafiya yake,sannan ko wane lokaci wannan layin zaizo kan mutum,ya shirya ko bai shirya ba idan layin yazo kansa,dolen sa ya tafi kuma yayi tafiyar da har abada babu ranar dawowar sa 😭
Allah ( SWT) yake cewa a cikin littafinsa mai tsarki: " Tabbas kowace rai sai ta dandana mutuwa,kuma sannan garemu ake mayar da ku" ( Ankabut '57")
Mutuwa dole ce akan kowa ma dayake raye a duniyar nan.shiyasa ba'a son mutum ya shagala da rudin duniya ko dadin ta wanda har zai Saka ya manta da makomar sa.
Da ace akwai wani wanda ya can-canci ya tsallake mutuwa ko ya dauwama a bayan kasa,to da fiyayyen halittane Annabi Muhammad (SAW),amma sai Allah ya tabbatar masa cewa" kai mai mutuwa ne,kuma lallai suma masu mutuwa ne "( zumar '30").
Lallai zafin fitan rai yana da wani irin radadi wanda babu mai saninsa saidai mamacin 😭
Zan mutu 😭
Zaka mutu 😭
Zaki mutu 😭
Duk duniyar nan babu mai tabbata a cikin sa kowa tafiya zaiyi kuma zai mutu,dukkan mu watarana zamu tattaru a gaban wanda ya halicce mu.
Daga lokacin da kazo mutuwa "dan Adam zai gane cewa ashe shi ba komai bane.kuma tun daga sannan zai fara nadamar lokutan rayuwarsa da s**a tafi wajen sa'bon Allah!!
Imamul Bukhariy ya ruwaito daga Nana Aisha (rta) tana bayar da labarin jinyar da manzon Allah (saww) yayi adakinta,har zuwa rasuwarsa.Tace :
" Hakika Manzon Allah ( SAW) ya kasance a gabansa akwai wata guga wacce akwai ruwa acikinta,yana shigar da hannayensa acikin ruwan sannan ya shafe fuskarsa dasu.yana cewa:
" LA ILAHA ILLAL LAH!! HAKIKA MUTUWA TANA DA RADADI!!"
Sannan ya chira hannunsa sama yana cewa:" ACIKIN TAWAGA MADAUKAKIYA !". ( A lokacin an bashi za'bi ne tsakanin ci gaba da zaman duniya,ko kuma komawa zuwa ga ubangijinsa).
Yana fa'dar haka har sai da aka karbi ransa sannan hannunsa ya karkato...
Allah kasa mu cika da imani 😭
©️ Aminu bbc center