27/04/2022
Hana Al-majiranci: Yi wa Karatun Al-Kur'ani Kafar Ungulu Ne Ko Gyara Kayanka, Ina Mafita?
Mutane sun kasu gida biyu a kan kurar da ta taso kwanakin baya game da mayar da mayar da al-majirai garuruwansu, wadansu suna gani wannan yinkuri ne mai kyau, a wani janibin kuma wadansu suna ganin yi wa Karatun Al-Kur'ani Kafar Ungulu ne. A wani bangaren kuwa, akwai wadanda ba sa wannan bangaren ba sa can. Kodayake, idan muka duba, kundin Tsarin Mulki ya raba madafun iko zuwa gida uku k**ar haka:
1. Kananan hukumomi
2. Jihohi
3. Tarayya
A wadannan rabe-raben za a ga cewa, jihohi da Tarayya su ne abin lura a wannan gaba.
Mene ne matsayar Tarayya a kan wannan lamari na mayar da al-majirai garuruwansu na asali? Ko shakka babu, Tarayya sun fito sun magantu a kan cewa a dakata da mayar da al-majirai zuwa garuruwansu na haihuwa. Waiwaye aka ce adon tafiya inji masu iya magana. Gwamnatin baya ta fito da tsari na killace almajirai da zamanantar da makarantunsu. Amma wannan gwamnatin ta Baba Buhari da ta hau shiru kake ji Wai malam ya ci shirwa.
Shin tsarin ya Sha ruwa ne ko kuwa yana nan an daga matashin kai an ajiye shi?
Mece ce Bara?
In an a ce bara, ana nufin ka je ka roki abin da ba ka da shi a wajen wani. A wani kaulin, bara tana faruwa ne sak**akon rashin wadata ne yake sa mutum ya je ya nemi abin da ba shi da shi a wajen mai shi don biyan bukata. Daga karshe, yanayi ko Canjin rayuwa ke sa a yi bara lokacin da ba ka da shi.