07/09/2023
KAIMA KANA CIKINSU?
Idan har baka cikinsu ya kamata ka/ki nema ma kanka/ki mafita.
Mafi yawan mutanen da suke zurga-zurga a social media fa duk 'yan "enjoying" ne, amma fa a ganinsu.
Jira kuji gaskiyar lamari...
A misali na siya "WAYA" da ku'dina, na saka mata "DATA" da ku'dina, nayi mata "CHAJI" da wutar NEPA da muka biya ko kuma da wutar "GENERATOR" da muka zuba ma fetur, ko kuma inje in biya ku'di a saka mun chaji, a haka kuma daga 'karshe sai nazo nayi amfani da "LOKACINA" na hau "ONLINE" na fara yawo kamar wani shaho, bani Facebook bani a whatsapp, idan tayi mun 'dadi har Instagram nake zagayawa inyo dubiya, a 'kalla sai in samu 1Hour ko 2Hours ina wannan kujiba kujibar, nine saka status da duba status, nine saka story da duba story, nayi fice wajen iya tagging da mentioning.
Alhali a cikin wannan lokacin dana 6ata akwai wasu wa'danda suna nan a saman social media 'din suna cinikayya, wasu suna ilmantuwa haka wasu suna can gefe 'daya suna bincike akan wasu al'amuran na yau da kullum wanda zasu amfanar da rayuwarsu, wasu kuma sune gefe sun hau jirgin siyasa suna tallata 'yan takararsu na siyasa, suna amsar 'yan chanji.
Kuna ganin bana ma kaina wauta kuwa? Idan wani yayi mun kallon sakarai mai 6annatar da lokacinshi tare da watsar da rayuwarshi a banza, zan iya cewa yayi laifi kuwa?
Haba gaye/gayiya ku duba da kyau fa ku gani, lokaci fa baya jiran kowa, kada ku bari 'kawa zuci da san sharholiya su kashe maku zuciya.
Da yawa akwai matasan da suke ciyar da kansu har su ciyar da wasu ta dalilin ribar da suke samu a social media akan ayyukan da suke a biyasu ko kuma siye da siyarwar da suke su samu riba.
Kar kace maza ka'dai, har matan ma akwai masu samun ribar da suke biya ma kansu 6u'katun yau da kullum kuma duka anan kan social media 'din da kai kuma ka maida dandalin gararanbarka.
Bari in gaya maku gaskiya masu irin wannan rayuwar, ba ku bane kuke "ENJOYING" da social media 'dinnan ba, ana dai yin enjoying har ayi earning daku.
-Developers na social media 'dinda kuke hawa.
-Masu sayar maku da wayoyin da kuke amfani dasu.
-Masu siyar da Data da masu siyar da chaja, harma da masu yin chaji.
Sune masu enjoying daku harma suyi earning daku, ku kuma kun tashi a 'kattin banja marasa sanin muhimmancin lokacinsu na rayuwa.
Allah ya ganar damu muhau hanyar enjoying da earning a social media, Amin.