15/08/2026
HUJJOJIN DA SUKE NUNA CEWA MAULIDI BIDI’A NE
Mutane da yawa suna cewa ana yin Maulidi saboda son Annabi ﷺ. To babu shakka, ƙaunar Annabi ﷺ wajibi ce. Amma tambayar ita ce: Annabi ﷺ ya yi Maulidi? Sahabbansa sun yi? Tabi’ai sun yi?
Idan ba su yi ba, me ya sa mu za mu mayar da shi ibada?
Allah ya ce:
﴿ٱلۡیَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِینَكُمۡ﴾
“Yau Na cika muku addininku.”
[Al-Mā’idah: 3]
Idan Allah ya ce addini ya cika, ba mu buƙatar ƙara masa wata ibada da Annabi ﷺ bai zo da ita ba.
Allah kuma ya ce:
﴿لَّقَدۡ كَانَ لَكُمۡ فِي رَسُولِ ٱللَّهِ أُسۡوَةٌ حَسَنَةࣱ﴾
“Lalle kuna da kyakkyawan abin koyi a cikin Manzon Allah.”
[Al-Aḥzāb: 21]
To idan da gaske muna son Annabi ﷺ, mu bi shi yadda ya yi, ba mu ƙirƙiri wata ibada da shi bai yi ba.
Annabi ﷺ ya ce:
«مَنْ أَحْدَثَ فِي أَمْرِنَا هٰذَا مَا لَيْسَ مِنْهُ فَهُوَ رَدٌّ»
“Duk wanda ya ƙirƙiro wani abu a cikin wannan al’amarin namu wanda ba ya cikinsa, to an mayar da shi.”
[Bukhari da Muslim]
Kuma ya ce:
«وَكُلُّ بِدْعَةٍ ضَلَالَةٌ»
“Kowace bidi’a ɓata ce.”
[Muslim]
Saboda haka, magana ba wai muna ƙin Annabi ﷺ ba ce. A’a. Muna son Annabi ﷺ ne, shi ya sa muke son mu bi Sunnarsa.
Annabi ﷺ ya rayu, ya koyar, ya yi ibada, ya rasu. Sahabbansa kuma sun bi shi sosai. Amma babu ɗayansu da ya yi bikin Maulidi.
Don haka idan aka ce: “Ina hujjar Maulidi daga Annabi ﷺ?” — ba za a iya kawo sahihin hadisi da yake cewa “ku yi bikin ranar haihuwata” ba.
Ƙaunar Annabi ﷺ tana cikin bin Sunnarsa, ba cikin ƙara masa ibadar da bai shar’anta ba.
Allah ya shiryar da mu zuwa ga gaskiya, ya sa mu mutu muna kan Sunnah. 🤲🏽