26/04/2025
Kana Matashi.. Ka dena kokarin burge kowa specifically ya'n matan nan, ka kashewa mindset da mafarkinka wannan kuɗi zaka ga yadda mutane da ya'n matan zasu bibiyeka.
Inda hali ka gujewa soyayya, in kuma ka afka ka ka dena renonta da Naira, soyayyar da aka gina da kuɗi da kuɗi kaɗai ake iya raya wannan soyayya, dan haka karka sa kanka a wannan rigima.
Ba wanda zai taimakeka ina tabbatar maka kai zaka tashi ka taimaki kanka, Wadanda s**a manta dakai mafarkinsu suke ginawa Kaima ka mantasu ka fuskanci mafarkinka, Karka sake yi wa wani ƙorafin mai yasa ya dena damuwa dakai, domin Kulawar dake zuwa bayan ƙorafi "pretending" ce kawai.
Ka yarda da kanka! zaki bai taɓa damuwa da abinda dabbobin ke cewa akansa, wanda ya yarda da kansa bai damuwa da cecekucen mahassadansa.
Cikar yarda da kanka shine "yin shiru yayin da ka gano har a zuci basa sonka, yin shiru yayinda s**a dariya akan mafarkinka, yin shiru yayin da suke gulmarka a gefe suna zaginka" inde baka manta mafarkinka to kawai kaci gaba da tafiya kai kaɗanka!