11/04/2023
TARIHIN DIWANIN Maulanmu Sheikh Ibrahim Niass R.T.A
Sheikh Ibrahim Inyass R.T.A Ya rubuta baitukan Diwanansa akan haruffan babbaku, Sannan ko wane diwani kasidun cikinsa sun tattaro haruffan babbaku (ko dai a kafiyoyinsu ko kuma a haruffan farkonsu).
Wani lokacin Shehu yana amfani da tsarin ابتثجح duba ga tsarin littattafan Lugga, Wani lokacin kuma yayi amfani da tsarin ابجد duba ga ma'anoni da asali da adadi.
Sheikh Balarabe Jega R.T.A ne ya tattaro Diwanai guda biyar, Da farko ya rubuto su ya taho da su Nigeria Ya nuna wa Sheikh Atiku R.T.A, Daga baya sai aka sami diwani na shida, Sai Sheikh Atiku yayi musu dan takaitaccen ta'aliki ya baiwa Alhaji Danjinjiri ya buga shi, da izinin Sheikh Ibrahim Niass R.T.A.
1- Taisirul wusuli.
2- Iksirus sa'adati.
3- Salwatush shujuni.
4- Authakul ura.
5- Shifa'ul askami.
6-Manasiku ahlil widadi.
Sheikh Sani Kafanga R.T.A ya sami Diwani na bakwai (Nurul Hakki).
7- NURUL HAKKI:- Sheikh Sani Kafanga R.T.A ya hada shi da wadancan shidan su ka zama bakwai, Ya hada su da taalikin Sheikh Atiku Sannan shima ya kara wani ta'alikin akai, Sannan Ya baiwa Alhaji Abdulyassari ya buga shima da izinin Sheikhu R.T.A a rubuce.
Sheikh Balarabe Gusau R.T.A shine ya zo da Diwanin Sheikh Ibrahim Niass R.T.A na karshe (Sairul Qalbi), Ya baiwa Alhaji Danjinjiri ya buga amma shi babu ta'aliki a cikinsa, Mai yiwuwa ko saboda wadancan da s**a yi ta'alikin na farko sun yi wafati ne? Wannan diwani shine na takwas.
8- SAIRUL QALBI: Bisa dukkan alamu Sheikh Ibrahim Niass bai gama shi ba yayi wafati, saboda akwai haruffan babbakun da ba'a yi musu kasidu ba.
Diwanin Kanzul arifina ana daukansa a matsayin diwani na tara amma a wajen jerawa shine na bakwai, yana kunshe da kasidu shida, amma ni bana daukansa a matsayin diwani mai zaman kansa saboda kasidun da suke cikinsa guda biyar daga ciki suna cikin diwanai biyar da suke gabansa, ta shidan ce kadai mai zaman kanta, ita kuma ba a kan bahri daya suke da sauran diwanan ba, Amma sirrin wadancan diwanan