DCDS Hausa

DCDS Hausa DCDS Hausa
Labaran Duniya

IRAN TA CE AMURKA ZA TA BAR GABAS TA TSAKIYAJagoran Ƙoli na Iran, Mojtaba Khamenei, ya bayyana cewa Amurka za ta tilasta...
28/09/2026

IRAN TA CE AMURKA ZA TA BAR GABAS TA TSAKIYA

Jagoran Ƙoli na Iran, Mojtaba Khamenei, ya bayyana cewa Amurka za ta tilastawa barin Gabas ta Tsakiya, yana mai cewa dakarun Iran sun yi wa abokan gabansu “munanan raɗaɗi”.

Khamenei ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin na ƙasar Iran a ranar Litinin, 28 ga Satumba 2026.

Ya kuma ce dakarun Iran sun tura sojojin abokan gaba daga ruwan kudancin Iran zuwa Tekun Larabawa, tare da cewa za su ci gaba da matsa musu har sai sun bar yankin.

Wannan furuci ya zo ne yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin farfaɗo da tattaunawar diflomasiyya domin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila.

Ku biyo shafinmu domin samun sahihan labarai da muhimman abubuwan da ke faruwa a duniya.

20/09/2026

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma'adinai 37 da s**a rasu Neja

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta MURIC ta buƙaci a tabbatar da adalci tare da biyan diyya ga iyalan masu haƙar ma'adinai 37 da s**a mutu yayin da suke tsare a hannun hukumar tsaro da kare fararen hula ta Najeriya, NSCDC, a Jihar Neja.

A wata sanarwa da shugaban MURIC na jihar Kano, Malam Hassan Sani Indabawa, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce ta damu da yadda mutanen s**a mutu bayan k**a su a wani samame da aka kai kan masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba.

MURIC ta ce idan zarge-zarge da ake yi wa hukumomin sun tabbata, hakan na nuna rashin ƙwarewa da rashin mutunta rayuwar ɗan'adam daga jami'an.

Ƙungiyar ta ce kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma yarjejeniyoyin kare haƙƙin bil'adama na duniya sun tanadi kare rayuwa da mutuncin mutanen da ke hannun jami'an tsaro.

Ta kuma nuna damuwa kan abin da ta kira yawaitar zarge-zargen take haƙƙin bil'adama da ake dangantawa da wasu jami'an NSCDC a sassan ƙasar.

A ƙarshe, ƙungiyar ta buƙaci a tabbatar da adalci ga mamatan tare da biyan diyya ga iyalansu.

20/09/2026

Da ɗumi-ɗumi: Babban Limamin Masallacin Ƙasa Sheikh Makari Yace An Zalunci Sheikh Tsawon Shekaru Biyar a gidan Yari bayan kuma Juya masa magana akayi a lokacin da Yake ƙoƙarin Kare Annabi Muhammadu SAW.

Babban Limamin Masallacin Ƙasa na Najeriya, Sheikh Ibrahim Makari, ya bayyana cewa tsare Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gidan yari na tsawon shekaru biyar zalunci ne, yana mai cewa an juya masa magana ne ƙiri-ƙiri.

A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, an hangi Sheikh Ibrahim Makari yana magana kan shari’ar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da kuma yadda aka tsare shi a gidan yari.

A cikin kalamansa, Sheikh Makari ya ce:

“Zalunci ne, zalunci ne, zalunci ne. Kuma muna barranta kanmu zuwa ga Allah daga zaluncin da aka yi wa Sheikh Abduljabbar da kuma yadda aka juya masa magana ƙiri-ƙiri.”

Shehun malamin ya bayyana cewa a baya an hana shi yin magana kan batun Sheikh Abduljabbar, yana mai cewa waɗanda s**a hana shi magana suna da babban nauyi a wajensa. Sai dai ya jaddada cewa, a cewarsa, an juya wa Sheikh Abduljabbar magana ne a lokacin da yake ƙoƙarin kare martabar Annabi Muhammadu (SAW).

Hakazalika, Sheikh Ibrahim Makari ya sha alwashin cewa yanzu zai shiga cikin maganar Yanzu Sheikh Abduljabbar domin ganin an yi adalci, tare da ƙoƙarin ganin ya samu fita daga gidan yari.

20/09/2026

Ma’aikatar Ilimi ta jihar ta umarci shugabannin makarantu da su haɗa kai da jami’an lafiya wajen gudanar da rigakafin tare da wayar da kan ɗalibai da iyaye.

Za a fara kashin farko na rigakafin daga 20 zuwa 24 ga watan Satumba 2026, sannan a gudanar da sauran alluran bisa tsarin da ma’aikatan lafiya s**a tsara.

Cutar mashaƙo tana saurin yaɗuwa wadda ke shafar hanyoyin numfashi.

Ana iya kamuwa da ita ta hanyar yawu, majinar mai ɗauke da cutar, musamman lokacin tari ko atishawa.

Hukumomin lafiya sun ƙara ƙoƙari wajen yin rigakafi da wayar da kan jama’a domin hana cutar ƙara yaɗuwa a makarantu da sauran al’umma.

https://aminiya.ng/mutum-332-sun-kamu-da-cutar-masha%c6%99o-a-gombe/?utm_campaign=shareaholic&utm_medium=copy_link&utm_source=bookmark

20/09/2026

Alhaji Sani Lawan Kofar Mata, ya taka muhimmiyar rawa a siyasar jihar a lokacin mulkin Malam Ibrahim Shekarau, ya rasu.
Ya kasance tsohon Darakta-Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, kuma yana daga cikin manyan ’yan siyasar da s**a yi fice a jam’iyyar ANPP a Kano a wancan lokaci.
Sani Lawan Kofar Mata ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da s**a yi wa gwamnatin Shekarau tasiri a harkokin siyasa, musamman a lokacin zaɓen 2007, inda rahotanni s**a bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu goyon bayan Shekarau a wancan lokaci.
Za ayi jana'izarsa a gobe Litinin da karfe 9 na safe, fatan Allah yaji kansa da rahama.

20/09/2026

Commander: Jama’ar Hadejia Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Gwamna Malam Umar Namadi

Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Jigawa, Salihu Muhammad Atafi, ya ce dimbin jama’ar da s**a halarci taron “One Million March Tinubu/Danmodi 2027” a Hadejia ya nuna cewa al’ummar garin da ma jihar Jigawa baki daya na goyon bayan Gwamna Umar Namadi.

Atafi ya bayyana hakan ne a yayin taron da aka gudanar a garin Hadejia a yau Lahadi, inda ya ce yawan mutanen da s**a halarci taron ya zarce yadda masu shirya taron s**a yi tsammani.

Ya ce duk da cewa an yi wa taron lakabi da “One Million Match”, yawan jama’ar da s**a fito ya sanya ya k**ata a kira taron da “Unlimited Match”, saboda yadda jama’a s**a yi cincirindo domin nuna goyon bayansu.

A cewarsa, taron ya kasance wata alama ta yadda al’ummar Hadejia da jihar Jigawa ke kallon shugabancin Gwamna Umar Namadi.

“Wannan ‘ya’ya ne s**a zo kafin mahaifinsu ya zo,” in ji Salihu Muhammad Atafi, wanda shi ne Commander na jam’iyyar APC a jihar Jigawa.

20/09/2026

Atiku ya ce rashin halartar taron na Majalisar Dinkin Duniya na iya yin tasiri ga hulɗar Najeriya da ƙasashen duniya, kuma "ƴan Najeriya na da haƙƙin sanin dalilin da ke hana Tinubu zuwa Amurka".

Ƙarin bayani - https://bbc.in/47dvdHS

19/09/2026
19/09/2026

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya bukaci a gudanar da cikakken bincike kan yadda aka yi matasa s**a mutu a hannun jami'an tsaro a jihar Neja. Tuni ma dai gwamnatin jihar ta Neja ta sanar da kafa dokar hana zirga-zirga.

Address

Kaduna
Kafin Hausa
741103

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DCDS Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share