07/07/2026
Wani mai bibiyar shafin Eagle Radio Bauchi, Yusuf Isa Abul Ihsan, ya bayyana hakan ne a sashen sharhi ƙarƙashin wasu hotuna da shafin ya wallafa, waɗanda s**a nuna yadda ƴan ƙungiyar Triple R ke ci gaba da gudanar da taruka domin nuna goyon baya ga jam'iyyar APC.
A cewarsa, lokaci ya yi da mutane za su fara tantance bambanci tsakanin hidimar al'umma da siyasa. Ya yi ikirarin cewa wasu daga cikin fitattun ƴan Kannywood da ake ganin suna tare da jama'a a baya, a yanzu sun koma kusantar masu mulki domin biyan bukatunsu.
Ya ƙara da cewa kowa na da ƴancin bayyana ra'ayinsa da kuma goyon bayan wanda yake so, amma bai kamata a ɗauka cewa duk abin da ake yi saboda al'umma ne ba.
Yusuf Isa ya kuma buƙaci jama'a su kasance masu buɗaɗɗen ido, su rika kallon aiki da sakamakonsa, maimakon hotuna da tarukan siyasa kaɗai.
A ƙarshen sakonsa, ya ce, "Baya ganin laifinsu (Ƴan Kannywood) neman na tuwo sukeyi. Al'umma kuma ba don su ake yi ba.