09/02/2026
SAKON GODIYA DA BANGAJIYA
Assalamu Alaikum
A madadin shugaban wannan Makaranta Madarasatu zikra Shehu Usman Bin Fodiy Danja, Imam Suleiman Sani Danja (Babban Limamin Jumuah na Garin Danja) Muna miƙa sakon godiya tare da bangajiya ta musamman ga dubban al’ummar da s**a halarci gagarumin taron Walimar Saukar Alkur'ani Mai girma na Dalibai guda 102.
Hakika halartar ku da goyon bayan da kuka nuna ya ƙarawa wannan taro armashi da nasara.
Muna miƙa godiya ta musamman ga manyan baƙi da s**a tallafa, s**a ba da gudunmawa, kuma s**a tsaya tsayin daka wajen ganin wannan taro ya gudana Cikin Nasara.
Cikin girmamawa da mutuntawa muna mika godiya ga:
1. Hon. Abdullahi Balarabe Dabai – Memba a Majalisar Wakilai ta Tarayya (Bakori/Danja Constituency).
2. Alh. Sani Sabiu – M.D/C.E.O, AS&S Alheri Bread Danja.
3. Alh. Aminu Lawal – Shugaban Katsina State Traders Union, reshen Karamar Hukumar Danja.
4. Alh. Adda’u – C.E.O, Rahamaniyya Bread.
5. Alh. Yazid Abubakar – Sarkin Fulanin Danja kuma wakilin Hakimin Gundumar Danja.
6. Alh. Sani Sunusi – Shugaban Kasuwar Tumatur ta Danja.
7. Alh. Mahmud Nuhu - M.D/C.E.O M,Lovers Special Bread
’Yan Kasuwar Filin Tumatur, da kuma sauran ’yan kasuwa na fadin Karamar Hukumar Danja.
Haka nan, muna mika godiya ga Malamai, Iyaye, Masu ruwa da tsaki, da dukkan al’ummar da s**a Sami halarta da kuma waɗanda ba su samu damar halarta ba amma s**a ba da gudunmawa ta hanyoyi daban-daban ta kuɗi, addu’a, shawara ko ƙarfafa gwiwa. Lallai gudunmawar ku ta taka muhimmiyar rawa wajen nasarar wannan gagarumin taro.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka muku da alheri, Ya ninka ladan duk abin da kuka bayar, Ya albarkaci rayuwarku da dukiyarku, kuma Ya biya ku da Gidan Aljannah.
Mungode ƙwarai da gaske. Allah Ya saka da alheri.