Zawiyar Maulana Sheikh Aliyu Umar Kaltugo R.T.A

Zawiyar Maulana Sheikh Aliyu Umar Kaltugo R.T.A Masoya Annabi zallah S.A.W

10/11/2024
 Insha Allahu Yau Talata 27/2/2024 Muna da Babban Bako da Zai Ziyarcemu a Garin Kumo,              ,  Zamuyi Magriba da ...
27/02/2024


Insha Allahu Yau Talata 27/2/2024 Muna da Babban Bako da Zai Ziyarcemu a Garin Kumo, , Zamuyi Magriba da Wazifa dashi a Jauroji Zawiyyah, sannan in Anyi Sallar Isha'i zai Gabatar da Majlisi insha Allahu!
Don haka Muke sanarwa Masoya Manzon Allah SAW Dake cikin Kumo da Kewaye, Allah ya barmu da Annabi Muhammad SAW

Via Aliyu Muhammad Tukur Kumo

MAULANA SHEIKH ALIYU UMAR KALTUNGO Radiyallahu AnhuAllah ya qara Kusanci Da ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM
26/02/2024

MAULANA SHEIKH ALIYU UMAR KALTUNGO Radiyallahu Anhu

Allah ya qara Kusanci Da ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM

MAULUD!     MAULUD!!     MAULUD!!!Amadadin Zawiyyar MAULANA Sheikh Aliyu Umar Kaltungo Radiyallahu AnhuMuna Farin Cikin ...
12/10/2022

MAULUD! MAULUD!! MAULUD!!!

Amadadin Zawiyyar MAULANA Sheikh Aliyu Umar Kaltungo Radiyallahu Anhu

Muna Farin Cikin Gayyatar Yan Uwa Masoya Manzon Allah Sallallahu ALAIHI WASALLAM

Zuwa Wurin Gagarumin Mauludin Manzon Allah Sallallahu ALAIHI WASALLAM

Tareda Jerin Gwano (Rali)

Wanda Za Ayi Kamar HAKA:----

RANA:-- Lahadi 20 RabiUl Auwal
Wanda Yayi Dai Dai Da
16-10-2022

Lokacin Jerin Gwano
Daga Qarfe 08:00am Zuwa 02:00pm

Lokacin Karatun Mauludin
Daga 08:00pm Zuwa Wayewar Gari Litinin

Allah Ya Bada Ikon Halarta
AMIN SUMMA AMIN

06/09/2022

TARIHIN ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA KASHI NA ARBA'IN DA BIYU (42)

2- Ayarin Fuzarah

Wannan ayari sun zo ne bayan Manzon Allah (SAW) ya dawo daga Tabuka su wajen goma sha wani abu ne, sun yi ikirari da Musuluncinsu. Manzon Allah (SAW) ya tambaye su game da garuruwansu, sai s**a yi kukan farin da ke addabarsu s**a ce “Ka roka mana Allah Ya ba mu ruwa ka nemar mana ceton Ubangijinka don ya nema mana cetonka. A nan ne Manzon Allah (SAW) ya tabbatar musu Allah kadai ake neman ceto a wurinSa, Shi ba ya nema a wurin kowa! Shi ne abin bautar da babu wani abin bauta sai Shi, Mai girma da Daukaka. Ya hau kan munbari ya roki Allah har sai da aka saukar musu da ruwa mai yawan gaske.

3- Ayarin Najran

Wani yanki ne da ya yi iyaka da Yamen kuma babban yanki ne yana da alkaryu 73. Suna da mayaka dubu 100, kuma suna kan addinin Nasara ne. Manzon Allah (SAW) ya aika musu da wasika yana kiransu zuwa ga Musulunci, sai s**a hadu s**a yi shawarar su aiki ayari ya je wurinsa a magance matsalar. Da s**a zo suna sanye da kayan kawa na alfahari da alharini da zobban zinari. Manzon Allah (SAW) bai yi musu magana ba sai wadansu manyan sahabbai s**a yi musu ishara da su je su cire zobban da kambunan, sai s**a aikata. Sannan ya yi musu magana ya kira su zuwa ga Musulunci amma s**a ki karba s**a ce mu masu mika wuya ne gabaninku. Sai ya ce musu Musulunci ai ya hana muku abubuwa uku:

-Bautar kuros (gicciye).

-Cin naman alade.

-Riyawar da kuke yi cewa Allah yana da da.

Sai s**a ce to wane ne misalin Isah? Sai Allah Ya saukar da wannan ayar a cikin Ali Imran: “Lallai misalin Isa a wurin Allah k**ar Adamu ne, an halitta shi daga turbaya, sa’annan aka ce masa ‘kasance’ sai ya kasance.” (Ali Imran: 59).

Bayan ya karanta musu har zuwa aya ta 61 sai ya nemi su zo a yi mubahala a ga mai gaskiya a cikinsu. Suna jin haka s**a nemi ya dan ba su lokaci sai s**a kebe suna shawara, s**a ce tabbas idan har Annabi ne kuma muka yi to babu wanda zai saura cikinmu sai ya hallaka, daga nan s**a amince su dai rika bayar da Jizya. Aka yarje musu kuma aka rubuta a rubuce kullin zaman amana da ’yancin yin bautarsu. Sai s**a ce, to, ka aika wani amintacce tare da mu. Sai Manzon Allah (SAW) ya aika Abu Ubaida Amir dan Jarrah (RA), shi ne ya sa ake kiransa da Amintaccen Wannan Al’umma.

4- Ayarin Da’ifa

Ya gabata an tsare mutanen Da’ifa bayan gama Yakin Hunain inda s**a ki fitowa a yi yaki, a karshe aka yanke shawarar a kyale su. Lokacin da Musulmi suke komawa ne Urwa dan Mas’ud Assakafi ya bi sawun Manzon Allah (SAW) kuma ya riske shi kafin ya shiga Madina, ya Musulunta sannan ya koma ga mutanensa, sun nuna k**ar suna sonsa daga baya s**a harbe shi ya rasu.

Wannan aika-aikar ta hana su kwanciyar hankali suna tsoron a kawo musu hari, sai s**a aiko Abdulyalil da wadansu mutum biyar daga madaukakansu.

Wannan aika-aikar ta hana su kwanciyar hankali suna tsoron a kawo musu hari, sai s**a aiko Abdulyalil da wadansu mutum biyar daga madaukakansu.

Manzon Allah (SAW) ya saukar da su kusa da masallaci suna jin karatun Alkur’ani kuma suna ganin ana yin Sallah, a cikin kwanukan da s**a yi Manzon Allah (SAW) ya kira su zuwa ga Musulunci ba su dai musulunta ba sai daga baya s**a nemi Manzon Allah (SAW) ya yi musu rangwame a kan wasu abubuwa, ma’ana a bar su su rika aikata su: su ne shan giya da zina da cin riba. Kuma kada ya sa su rusa babban gunkinsu Lata kuma ya yafe musu yin Sallah kuma kada ya sa su rusa gumakansu da hannuwansu. Sai Manzon Allah (SAW) ya ki amma ya yarda kada su rusa gumakan da kansu. Sun musulunta Usman dan Al-As shi ne dan karaminsu ya kasance ya koyi karatun Alkur’ani a wurin Annabi (SAW), idan ya same shi yana barci sai Abubakar (RA) ya karantar da shi kuma ya boye haka ga mutanensa a haka ya haddace wani abu mai yawa. Da s**a musulunta sai Manzon Allah (SAW) ya wakilta shi a kansu saboda kwadayinsa ga karatun Alkur’ani da neman ilimin addini.

Bayan ayarin ya koma sai s**a boye imaninsu gudun yaki, s**a shaida wa mutanensu cewa sun hadu da kausasawa da takobi a fili, s**a fadi sharuddan da aka yi musu da hanin giya da zina da sauransu ko kuma a yake su. Da s**a ji haka sai s**a shiga shirin yaki cikin kwana biyu ko uku sai dai ko’ina ba su kai ba Allah Ya jefa tsoro a zukatansu s**a ce wa ayarin ku koma ku ce mun yarda da abin da ya yi umarni kuma mun mika wuya. Sai mutanen s**a ce musu ai mun gama komai dama mun musulunta, daga nan duk Sakifawa s**a musulunta.

Manzon Allah (SAW) ya aika Khalid dan Walid da Mughira dan Shu’uba Assakafi da wadansu mutane zuwa Da’ifa su rusa Allata, s**a je s**a rusa ta da gininta.

5- Ayarin Banu Amir

Su uku ne s**a zo wurin Manzon Allah (SAW) kuma su ne shugabannin mutanensu kuma shaidanun mutanen, kuma su ne dai s**a yaudari sahabbai a Bi’iri Ma’unah. su ne: Amir dan Dufail da Urbad dan Kais da Jabir dan Aslam.

Sun zo ne da nufin kashe Manzon Allah (SAW) da s**a zo wurinsa ya kira su zuwa Musulunci, sai Amir ya ce: “Ina ba ka zabi cikin abu uku: Mutanen Sahlu su zama naka ni kuma mutanen Mudar. Ko in zamo Khalifa a bayanka. Ko in yake ka ni da Gadafan.” Sai Manzon Allah (SAW) ya kore dukkan wadannan ya ce: “Ya Allah! Ka isar mini ga Amir kuma Ka shiryar da mutanensa.” Bayan su Amir sun juya kan hanyarsu ta komawa ya sauka gidan wata ’yar uwarsa, Allah Ya aiko masa da annoba ya fara kwara amai, ya sa aka kawo masa dokinsa ya hau ke nan ya mutu a kansa. Shi kuma Urbad tsawa ta kona su shi da rakuminsa, shi ne fadar Allah: “Kuma aradu tana tasbihi game da gode maSa, da mala’iku domin tsoronSa. Kuma Yana aiko tsawarwaki, sa’annan Ya samu wanda Yake so da su, alhali kuwa su, suna jayayya a cikin (al’amarin) Allah, kuma Shi ne mai tsananin (shirya) hila.” (Ra’ad: 13).

Mu’ila dan Jamil shi ma dan kabilarsu ce kuma ya ruwaito wannan kissar ya je wurin Manzon Allah (SAW) ya musulunta yana dan shekara ashirin ya yi mubaya’a ya mika masa rakuminsa, ya rayu tsawon shekara dari a Musulunci ana kiransa da ma’abocin harshe biyu saboda fasaharsa.

6- Ayarin Banu Hanifa

Sun zo Madina su goma sha bakwai a cikinsu akwai Musailamatul Kazzab, sun sauka gidan wani mutum sannan s**a zo s**a musulunta. An ce har da Musailama, a wata ruwayar kuma an ce bai je ba, ya ce sai idan Manzon Allah (SAW) ya yarda ya zama Khalifa a bayansa. Da ma Manzon Allah (SAW) an nuna masa a mafarki fitowar makaryata a bayansa. Da Musailama ya gabato wurinsa yana rike da gutsuren ganyen dabino a hannunsa, ya tsaya cikin sahabbai. Bayan Manzon Allah (SAW) ya yi magana sai Musailama ya ce: “Idan ka so ka bar wannan lamarin tsakaninka da mu, kuma ka sanya shi gare mu bayanka.”

06/09/2022

TARIHIN FATIMA YAR ANNABI MUHAMMAD SAW KASHI NA HUDU (4)

Ranar Shahadar 'Yar Manzo, Sayyida Fatima al-Zahra (AS)

Abubuwan da s**a faru bayan Annabi (SAW), da s**a hada da cutar da al-Zahra (AS) sun kara zafafa mata ciwo da takaici, ta yadda har sai da s**a bar ta a kwance. Ta saura cikin jinyar matsanancin rashin lafiya har tsawon kwanaki arba'in.

Duk da haka, a karshen rayuwarta ta nuna alamun k**ar ta warke, domin ta tashi ta sa 'ya'yanta Hasan da Husaini (AS) s**a yi wanka, ta sa musu tufafinsu, sannan ta bukace su da su je su ziyarci kabarin Kakansu Manzo Allah (SAW).

Duk da wannan alama na samun sauki, ashe ita shiri take yi na haduwa da mahaifinta; sai ta bukaci Asma'u bint Umais da ta debo mata ruwan wanka, sai ta yi wanka ta sa mafi kyawun tufafinta.

Yayin da ta ji kusantowar ajali sai ta bukaci Asma'u da ta yi mata shimfida a tsakar daki, sai ta kwanta tana mai fuskantar alkibla. Sannan sai ta sa Asma'u da Ummu Aiman da su kira mata Imam Ali (RA). Da ya zo sai ta ce masa:

"Ya kai dan baffa!, ina jin cewa kuma ni na zo karshe. Ba na jin wani abu face cewa ni zan hadu da babana a 'yan sa'o'in nan. Ina so in yi maka wasici da abin da ke cikin zuciyata".

Sai Imam ya ce mata: "Yi wasici gare ni da abin da k**e bukata 'yar Manzon Allah", sai ya zauna daidai kanta, ya hori wadanda ke cikin dakin da su fita. Sai ita kuma ta ce masa:

"Ya dan baffa, ba ka taba samu na da karya ko cin amana ba, kuma ban taba saba maka ba tun da ka zauna da ni".

Sai Imam (RA) ya ce: "Allah Ya sauwaka, ai ke ma kin sani, kin fi biyayya, kin fi takawa, kin fi karimci kuma kin fi tsoron Allah a kan in zarge ki da saba min. Hakika rabuwa da ke da rashinki sun tsananta gare ni. Sai dai haka wani abu ne da ba makawa kansa. Wallahi kuma kin sabunta min musifar rabuwa da Manzon Allah (SAW), kuma hakika wafatin ki da rashin ki sun girmama Inna Lillah Wa Inna Ilaihi Raji'un! Wannan musifa me ya fi ta daga hankali da zafafa rai da bakin ciki!! Wallahi musifa ce da ba ta da makoki, kuma bakin ciki ne da ba shi da masauyi.".

Sai duk s**a yi ta kuka na wani lokaci, sannan sai Imam Ali (RA) ya k**a kanta ya kai kirjinsa ya rungume ta ya ce: "Fadi wasiyyar da k**e so, lallai za ki same ni mai cika ta, zan aiwatar da duk abin da ki ka h**e ni da shi".

Sai Fatima (AS) ta ce:

"Allah Ya saka maka da alheri, Ya kai dan baffa!, da farko ina maka wasici da ka auri 'yar 'yar'uwata Umamah (1), a baya na, domin ita za ta kasance ga 'ya'yana k**ar ni; domin mata dole ne ga maza.".

Har ila yau ta ci gaba da ce masa:

"Ina yi maka wasici da kar (ka bar) daya daga cikin wadannan da s**a zalunce ni ya halarci jana'izata, kar ka bar waninsu ya yi salla a gare ni. Ka bisne ni da daddare, lokacin da idanuwa s**a natsu kuma gannai s**a yi barci (2).

Sai ta cika wasiyyarta

Fatimatul-Zahra (a.s.) ta yi sallama da Ali (RA) da 'yan gidanta, aka dauke ruhinta mai tsarki zuwa gidan dawwama da ni'ima. Sai mai shela ya yi shelar cewa Fatima ta bar duniya sai Madina ta dauki zafi, zukatan muminai s**a buga saboda rasa bangaren Manzon Allah da reshen Annabci. Jin wannan labari, sai matan Banu Hashim, na Muhajirai da Ansar s**a taru, mutanen Madina s**a yi dandazo a kofar gidan Ali; masu hudubobi s**a shiga tunatar da ranar rasuwar Manzo (SAW) a gidan Fatima da kalmomi bakin ciki.

Taron jama'a na jira su ga an fito da al-Zahra (AS) zuwa makabarta; sai dai Imam Ali (RA) ya umarci Salman - ko kuma Abu Zarri, bisa sabanin ruwaya - da ya sallami mutane, ya ce musu Fatima ta hana mutane su shaida jana'izarta kuma kar kowa ya shiga wajen gawarta. Jikinta mai tsarki ya saura har sai da idanuwa s**a dauke sannan Imam Ali ya dora ta a kan wata makara da Asma'u bint Umais ta yi shi; sannan shi, Hasan, Husaini, Ammar, Mikdad, Akil, Zubair, Abu Zarri, Salman, Baridah da wasu mutane daga Banu Hashim s**a raka jikinta mai tsarki zuwa Makabartar Baki'a s**a bisne ta a can, s**a kuma boye duk wata alamar kabarin don kar mutane su gane.

An ruwaito cewa lokacin da Imam Ali (RA) ya saka Fatima a cikin kabari wani bakin ciki ya kara lullube shi, rabuwa da ita ya tsananta gare shi, matsayin ya yi matukar girmama a gabansa, sai ya fuskanci kabarin Manzon Allah (SAW) don ya isar da kukansa, yana mai nuna irin kaunar da yake mata da cikawa Maihaifinta alkawari da bakin cikin rabuwa da ita da zafin abin da ya same shi tare da ita.

An ruwaito cewa a wannan lokacin Imam Ali (RA) ya fuskanci inda Manzo (SAW) ya ke ya yi sallama a gare shi da kuma bayyana masa irin halin da s**a shiga ciki bayansa da irin bakin cikin da ya same su sak**akon abubuwan da al'ummarsa s**a aikata musu.

Haka Fatima al-Zahra ta rufe rayuwarta, don ta fara rayuwar dauwama a Firdausi, kuma don ta rayu rayuwa har abada a lamirin tarihi da duniyar Musulunci a matsayin abin koyi da zukata ke daukaka da ita.

Amincin Allah ya tabbata a gare ki, Ya al-Zahra, ranar da aka haife ki, ranar da kika yi shahada da kuma ranar da za a tashe ki kina rayayyiya.

Address

Emir Palace
Gombe

Telephone

234

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zawiyar Maulana Sheikh Aliyu Umar Kaltugo R.T.A posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The University

Send a message to Zawiyar Maulana Sheikh Aliyu Umar Kaltugo R.T.A:

Share