05/06/2020
BARKANMU DA ASUBA
Labaran Safiyar Jumma'a 05/06/2020CE - 13/10/1441AH. Cikakkun labaran
An samu karin mutane 350 da s**a kamu da Coronavirus a Najeriya, jimilla 11,516.
Gwamnatin tarayya za ta gina wa 'yan gudun hijra 500 a jihohi 4 na Arewacin Najeriya.
Gwamnatin jihar Katsina ta sake bude kasuwanni ta umurci ma'aikata su koma bakin aiki.
'Yan jam'iyyar APC 10,000 sun sauya sheƙa sun koma PDP a jihar Kwara.
Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da cewa duk masu dauke da Coronavirus a jihar sun warke.
'Yan bindiga sun kashe manoma 13 a wani fito-na-fito da s**a yi a jihar Zamfara.
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta k**a wata mota makare da giya a jihar.
Gwamnatin Tarayya za ta biya naira bilyan 1.7, ladar zanen taswirar sabon titin saukar jirage a filin Abuja.
Majalisar Dattawa na binciken yadda dala bilyan 3.3 da s**a bace a CBN.
Kasashen duniya sun caccaki Amurka kan kashe George Floyd.
Mutum 7,000 sun tsere daga sansanin 'yan gudun hijira a Nijar.