Kulliyyatul Qur'aan, Yola

Kulliyyatul Qur'aan, Yola This is a Qur'aan memorization school page aimed at enlightening the general public about the school

07/02/2026

SANARWA TA MUSAMMAN

08/07/2025

Wannan ɗalibi da kuke gani Allah Ya jarabce shi da rashin gani na idanu, amma kuma Allah Ya masa baiwa na ƙoƙari sosai wajen iya karatun Alqur'ani kamar yadda kuke ji. Muna fata Allah Ya sanyawa rayuwarsa albarka. Kuma Ya bashi damar kammala haddan Qur'an

10/05/2025

Karatun daga bakin Ja'afar Yakubu

08/02/2025
05/11/2024

ALHAMDULILLAH

Allah muke roƙo da Ya kawo mana sauƙi cikin dukkan lamuran mu.
30/07/2024

Allah muke roƙo da Ya kawo mana sauƙi cikin dukkan lamuran mu.

Dama domin 'ya'yanku
05/07/2024

Dama domin 'ya'yanku

01/04/2024

Mu shaƙata da karatun Al-Qur'ani mai girma.
Fatan kowa ya sha ruwa lafiya

01/04/2024

Alhamdulillah. Bayan fiye fa shekaru 3, Allah Ya bamu daman ƙwato wannan account ɗin namu duk da mun riga mun buɗe Sabo. Da fatan Allah Ya ƙarɓi ibadun mu.

Alhamdulillah. Da fatan Allah Ya amsa mana ibadun mu Ya kuma karɓa mana azumi da muke gabatarwa
27/03/2024

Alhamdulillah. Da fatan Allah Ya amsa mana ibadun mu Ya kuma karɓa mana azumi da muke gabatarwa

RIGE_RIGEN YIWA YARAN ISLAMIYOYI WALIMAR SAUKAR AL-QUR'ANI YA HAIFAR MANA DA MATSALOLIA gaskiya karatu yanzu ya zama abi...
29/12/2021

RIGE_RIGEN YIWA YARAN ISLAMIYOYI WALIMAR SAUKAR AL-QUR'ANI YA HAIFAR MANA DA MATSALOLI

A gaskiya karatu yanzu ya zama abinda ya zama musamman a kasashen Hausa

Saboda son zuciya dake tattare da wasun mu dalibai da wasu daga cikin iyayen mu da kuma Wasu malaman ISLAMIYOYI

Gaskiya na zabi wannan maudu'i ne saboda illa da hakan ke haifarwa yayi yawa

★Bari mu ga wasu daga cikin dalilan da yake sa wasu Malaman islamiyoyi ke gaggawa don ganin sunyi Masu walima

1-Azazzalawan iyaye da gaggawa wajen ganin yaransu sun sauke al-Qur'ani

2-Cire Yara daga duk islamiyar da ba a yima Yara walima duk shekara

3-San abin duniya daga wasu daga cikin Malaman

4-Rashin me da hankali a kan karatu

Wadannan wasu ne daga cikin dalilan da s**a sa wasu islamiyoyin mu suke tunkuda Yara a karatu don ganin anyi sauka da wuri



1- A al'adar ƙasan Hausa kashi saba'in (70%) na Yaran da ake yima walima basu ci gaba da karatu musamman (MAZA)

To zaka ga yaro ya bar islamiya bayan sauka amma baze iya karantar da wani al-qur'ani ba

2-Zaka ga tun ana sauran wata daya ko biyu za a yankan ma yaro ayoyin da ze karanta ranar walima
Amma in ranar tazo ya hau mimbari se ka ga yana Jan ayar itama tana Jan shi

3-Hakan ya janyo mutane da dama basu San darajar karatu ba sun dauka makarantun da ake walima akai akai sunfi karatu

4-Kuma hakan ze janyo karancin kwararrun malaman da zasu karantar
Kuma su rike islamiyoyinmu a nan da wasu shekaru Masu zuwa

★Shawarwari ga
Iyaye
Malamai
Da Kuma mu dalibai akan wannan mas'alar



1. Ya kamata ku Zama Masu taimakama malamai wajen kula da karatun Yara ta hanyar hada Masu extra time table da zaku dinga duba Masu darrusan da ake Masu a Makaranta da kara Masu haske akan ababen da basu fahimta ba a Aji

2-Ya kamata iyaye su tabbatar suna tura yaransu Makaranta a kan lokacin da hukumar Makaranta ta ajiye na zuwa Makaranta

3-Ya kamata iyaye Sufi bada muhimmanci wajen lalubar wace Makaranta aka fi karantarwa ba Wai makarantar da akafi yima Yara walima ba

4-Siya ma Yara duk abinda suke bukata na karatun

5-Nuna ma Yara a shirye kuke Ku kashe Masu ko nawa ne matukar kuna da hali don ganin sunyi karatu

6-Bama malamai cikakken goyon baya don su karantar da Yara



1-Muji tsoron Allah mu mai da hankali akan karatunmu

2-Mu dage da rokon Allah ya fahimtar damu ababen da ake koya mana

3-Mu girmama malamanmu



1-Kuji tsoron Allah Ku kawar da kai daga ababen da ake samu lokacin walima

2-Duk Wanda ya bude islamiya ya kamata ya zama yana da tsarin da yake tafiyar da karatunsa akai kuma karya bari wani yana juya akalar karantarwarsa

3-Ya dinga samun lokaci Koda sau daya ne a duk bayan wata uku yana gayyatar taro yana tattaunawa da iyayen yara don in akwai wata matsala anan yakamata atattaunata a samu mafita

4-Kada ayi ma yaro sauka har se ya sauke alqur'ani sauka na haqiqa ta yanda duk Inda aka bude masa ze karanta babu fargaba kuma babu gargada

:

1. A kalla ya haddace arba'una Nawawi a bangaren hadisi

2. A bangaren tauhidi ha sauke usulussalaasa

3. A bangaren Tajwidi ya sauke kuma ya haddace tuhfatul atfaal

4. A bangaren fiqhu ace ya sauke kuma ya San akhdariy yadda ya kamata

5. A bangaren lugah ace ze iya rubuta wasika da larabcin

6. A bangaren sirah ace ya kammala Khulasatun nuurul yaqiin na farko

7. Sannan dole ya kasan ce yana da hadda karancin izu biyu

8. Ranar waliman iyayenshi ne zasu dauki qur'ani su bubbude mai duk Inda suke so ya karanta a ƙalla gurare biyar

bawai ayoyi za a yankan mai yake yafi practice ba
Wallahi duk makarantar da ta dauki wannan tsari kuma tasa shi a cikin tsarin makarantar

kuma duka iyaye su rattaba hannu a wannan to a walimar su na farko za ayi mamakin irin hazikan Taliban da zasu samu duk da dai nasan baza suyi yawa ba amma ai da haihuwar yuyuyu gwara daya kwakkwara

Kuma da ace irin wannan tsarin malamanmu s**a yi amfani dashi tun muna islamiyah wallahi da yanzu mun wuce haka nesa ba kusa ba
Ina rokon Allah ya bama malamanmu ikon amfani da wannan shawarwari domin kannanmu Masu tasowa
Daga
ALMALIKI UKASHA NURA BIN DAUD GASHUWA

Address

Jimeta

Telephone

+2348032653619

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kulliyyatul Qur'aan, Yola posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The University

Send a message to Kulliyyatul Qur'aan, Yola:

Share