11/12/2023
Wani Bawan Allah yayimin tambaya wai meyasa yan IZALA ke ganin kamar su ne kadai zasushiga aljannah a ranar alkiyama??
Amsa Shine: ๐
Zaka shiga aljannah idan kabi Allah da manzon Allah kuma kayi aiki irin na yan aljannah, sai Allah ya gafarta ma yayima rahama.
Ko kana acikin IZALA idan baka bin Allah da manzon Allah, idan kabi son zuciya, kayi aiki irin na yan wuta to ko shakka babu zakashiga wuta.
Kenan kasancewarka dan IZALA bazai hanaka shiga wuta ba har sai kabi Allah da manzonsa.
Kasancewarka dan DARIKA ba zai sa kashiga wuta ba matukar kabi Allah da manzon Allah ka bautata wa Allah shikadai batare da yimasa kishiya ba.
Saboda haka mudaina ruduwa da kungiya ko jinin malanta, WALLAHI duk inda kake, ko waye mahaifinka, ko kai jinin waye, duk karatunka duk iliminka wallahi sai kabi Allah da manzon Allah, kayi aiki irin na yan aljannah sannan zakashiga aljannah.
Manzon Allah saw yana matukar son NANA FADIMA, yarsa ce, kuma yace tsoka ce acikin jikinsa. Amma kuma annabi yace da ita wallahi a ranar alkiyama bazai iya ceton ta daga azabar Allah ba, har sai ta bi Allah anan duniya ta bautata masa.
Manzon Allah fa ๐ค
To ballantana wani shehi ko gausi ko malami.
Allah ya gafarta mana AMEEN.
Albashirmuhammad