04/05/2022
SAKO ZUWAGA YAN MATA AKAN KWALLIYAR SALLAH (01)
ANNABI S.A.W YACE:
Akwai Nau’i Biyu Na Yan Wuta Ban Gansu A Zamani Na Ba. Sai Annabi S.A.W Yace Na Farko, Wasu Mutane Ne Tare Dasu Akwai Bulala Ko Dorina Kamar Jelar Shanu, Suna Dukan Mutane Da Ita: Sannan Na Biyu; Mata Ne Sun Sanyan Tufafi Amma Tsirara Suke, Karkatattu Masu Karkatarwa, Kawunansu Kamar Tozon Rakumi Karkatacce, Bazasu Shiga Aljanna Ba, Kai Bama Zasuji Kamshin ta Ba, Alhali Kuwa Ana Jiyo Kamshin ta Tun Daga Tafiyar Nisan Kaza Da Kaza.”
Muslim Ne Ya Ruwaito Kuma Sheikh Muhammad Nasiruddin Al-albaniy Ya inganta Shi A Cikin Sahihul Jami’u, Hadisi Na 2,128.
Jama'a Kusani Cewa Sallar Idi Ba Wata Gargajiya Bace, Ibadace Da Allah Ya Shar'anta Ta Ta Harshen Fiyayyan Halitta Annabi Muhammad Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A Gareshi, Ita Ko Ibada Anayinta Akan Yadda Aka Tsarata Ne, Allah Ya Karbi Ibadarmu Yasa Ayi Sallah Lami Lafiya Ya Tsaremu Ya Tsare Mana Imaninmu.