06/11/2025
DUK MAI SONKA DA GASKIYA DOLE WATARAN YAYI YABO WATARAN YAYI S**A INDAI YANA SO KU HADU A ALJANNA YAU DAI YABONE
Hakika Abunda Sen. Barau I. Jibrin yayi na Yunkurin sabunta masallacin matafiya wanda akafi sani da masallacin , Yunkurine na ginawa kansa gida A Aljanna, kuma Alamace ta cikakken Imani, kuma ina kira ga Sauran jagorari suyi koyi dashi.
Ga Hujja daga cikin Al-Kur’ani mai girama da Hadisan Manzon Allah s.a.w
Acikin Suratu At-Tawbah aya ta (9:18) Allah madaukakin sarki yana cewa
إِنَّمَا يَعْمُرُ مَسَاجِدَ اللَّهِ مَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ...
Ma’ana: “Lalle ne waɗanda suke ginawa (ko kula da) masallatan Allah su ne waɗanda s**a yi imani da Allah da ranar ƙarshe...”
Wannan aya tana nuna cewa gina masallaci alama ce ta cikakken imani da kyakkyawar niyya ta ibada. “Ya’muru” a nan na nufin ginawa, ko gyarawa, da kula da masallaci.
Hujja daga Hadisan Manzon Allah s.a.w
1. Hadisin Uthman bn Affan (RA)Acikin littafin – Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim
قال رسول الله ﷺ:
"من بنى لله مسجداً بنى الله له مثله في الجنة."
Ma’ana: “Wanda ya gina wa Allah masallaci, Allah zai gina masa makamancin sa a Aljanna.”
(Bukhari, Hadisi na 450; Muslim, Hadisi na 533)
Amma wanda ya gina don neman Yardar Allah ba don isaba Allah ya sakawa Sanata Barau da Alkhairi ya kuma biya masa bukatarsa ta Alkhairi A duniya da lahira
Barau I. Jibrin
Dan Afirka
Saminu Uba Maiturare
Shiek Yusuf Abu Sumayya
Auwal Uba Maiturare
Ishaq Adam Rijiyar Zaki
Basiru Yusuf Shuwaki
DSports