08/08/2022
Labbaika ya rasulullah
Labbaika Ya Hussain.
Labbaikum ya Ahlul bait
Labbaikum ya As'habu rasulullah
Imam Anas
Haƙiƙa Imam Hussaini bana wata ƙungiya bane ita kaɗai, na dukkan Musulmai ne shi gaba ɗaya dan haka muna takaici da alhini akan irin kisan gillar da akayi masa a rana irinta yau.
AMMA BABU LAIFI.
Waɗanda s**a wayi gari, da Azumi tabbas sun aikata sunnah babba, domin ta tabbata daga Ma'aikin Allah ﷺ, yanayin Azumi duk goma ga watan Ashura saboda a ranar ne Allah ya tseratar da rundunar Annabi Musa daga sharrin Fir"aunan Misrah, ibada ce tun tuni domin ta samo asali a tarihin musulunci.
Sannan kuma babu laifi ka nuna baƙin cikin ka tare da alhini akan kisan gillar da akayima Imam Hussaini ɗin a rana irin ta Yau, shima kayi koyi da Ma'aikin Allah ﷺ, domin har hawaye yayi a lokacin da Mala"ika Jibrilu ya kawo masa saƙon za"a shahadantar da jikinsa kuma ɗaya daga cikin samarin gidan Aljannah tare da ƙasar gurin a hannun Mala'ika Jibrilu, kunga abu ne a bayyane basu haɗu da juna ba, sai mutum ya haɗa duka.
Amma kuskure ne, dan kaga wasu suna baƙin ciki kai kuma ka rinƙayin murna ko ka rinƙa nuna baka damu ba, gaskiya kuskure ne babba kuma bakayima ma'aikin Allah ﷺ, kara ba, ya za'a kashe ahalin gidansa, amma kana nunawa wai bai dace a nuna baƙin ciki ba, kana ƙalubalantar mutanen dakeyi bai dace ba, babu laifi kace sun zaƙe da yawa, wannan kuma daban su haka s**a fahimci addinin babu ruwanka dasu, amma ba hurumi bane kai kuma kayi murna saboda ka baƙanta musu sam bai dace ba, ka kuma aikata bidi'ah, dan haka karka damu da kowa kayi abinda ka fahimta suma ka barsu suyi abinda s**a fahimta ƙalubalantarsu ba naka bane, garin ƙalubalantarsu ɗin sai ka saki hanya baka sani ba.
Daga ƙarshe dai mun sani Imam Hussaini ba ƙasƙanci bane a gurinsa dan an shadantar dashi, ɗaukaka ce, domin kusan dukkan manyan Sahabban Ma'aikin Allah ﷺ, suma shahadantar dasu akayi dan haka su bayin Allah ɗaukaka ce a gurinsu saboda Aljannah tafi musu komai kuma sun samu tun a duniya.
Muna roƙon Allah ya ƙara la'antar waɗanda s**a shahadantar da jikan Ma'aiki saw