18/06/2020
MAHUKUNTA A SAKE TUNANI
A Cikin Wannan yanayi da muka tsinci kan mu hakika rayuwa tayi kunci! Fita neman abinci ma an ware ranaku kusan 50% na Al’umma sai an fita za a samu abin ciyar da iyali, haramta goyo a mashin a Wannan yanayi tabbas an kuntata wa Al’umma, amma fa ku sani hanya ce dodar ta nisanta jama’a da Gwamnati.
Wani idan yaje kasuwa abinda ya samo Bai taka kara ya karya ba, rage masa hanya za’ayi a mashin ya tsira da kudin aljihun sa wanda dasu zaiyi maleji a ciyar sa iyali, idan zai biya kudin adaidaita wallahi da wahala su isa yaje Gidan saboda suma sun nunka kudin saboda yanayi da aka fada.
Allah ka ceci Malam talaka