08/11/2015
KA TABA YIN ZINA ?
Zina tana cikin manyan laifuffuka, wanda
dukkan shariun da Allah taa'la ya saukar sun
hadu akan haramcin zina,
Al kur'ani mai girma da Sunnar Annabi saw,
da dukkan Malamai sun hadu akan haramcin
zina,
Kofofin zina guda biyar ne
1- Kallo zuwaga Abinda Allah ya Haramta
2- Shigar batsa
3- Kalaman Batsa
4- kebancewa da matar da ba muharrama ba,
5- Shaawa Mai karfi babu aure
Allah taala yace: " kada ku kusanci zina"
Manzon Allah saw yace : Mai zina ba zaiyi
zina ba, yayin da yake zina, sai an cire masa
imani.
Abdulllah Dan Mas'ud Ra yace :
Duk
Al'ummar da take zina, ta jawo wa kanta
fushin Allah, da halaka.
Musulunci yayi umarni da tsare abubuwa
biyar, sune : Addini, Dukiya, Rayuka,
Hankali, Mutunci, Nasaba, amma zina ita
kadai, tana rusha wadannan duka,
Hukuncin mazinaci, mai aure kisa ta hanyar
jifa, mara aure Bulala dari da daurin shekara.
Ana tabbatar da zina ta hanya uku, shedu
guda hudu, Mutun yayi ikirari da kansa,
samun mace da ciki, babu aure, ko shubha.
Bisa sharudda da aka sanyawa ko wanne.
Zina wata babbar musifa ce da bala'i da
dukkan sharri, da take ruguza al'umma, take
wargaza iyali, take tarwatsa gari, take rushe
mutunci, take jawo karayar tattalin arziki, da
fatara, da tsiya, da annoba, a cikin rayuwar
dai dai ku, da gidaje, da unguwanni, da
gururuwa, da kasashe, da duniya baki daya,
Zina itace cikakkiyar fitsara, a cikin zina ake
samun dukkan sharri kamar :
1- Raunin Addini
2- Raunin Akida
3-Karancin Imani
4- Rashin kunya
5- Rashin kishi
6- Rashin mutunci
7- Rashin kwarjini
8- Rashin hasken fuska
9- Duhun zuciya
10- Rashin kima
11- Rashin Nagarta
12-Rashin Nutsuwa
13- Rashin Amana
14- Fushin Allah
15- cikawa babu imani
16- Azabar Allah
Allah ya tsare mu da zuriyar mu, da dukkan
al'ummar musulmi daga afkawa zina,
wadanda suke yi Allah ya shirya
JSM ONDO