10/02/2022
Duk Yawan Matsalar Kasarmu Nigeria to India ta Ninkata Matsala Sau Dari Biyu Cewar Marigayi Dan Masanin Kano
Tabbas Ni Na Yarda da Wannan Magana Bayan Nazari Gami da Wani Bincike da na Aiwatar
Cikin Binciken Na Samu Tarihi Cewa Mahat Ma Ghandi Na Kasar India Yayi Gwagwarmayar Samuwar Yancin Kasar, , A Lokacin Yana Fadin Cewa Nan Gaba India Zata Zama Kasar da Ba ta Zub da Jini Ba
Hakika India a Shekaru Masu Yawa Baya Sunsha Fama da Matsaloli Sedai Sannu a Hankali Sun Dukufa Sun Hada Kawuna Sun Hada Karfi da Karfe, Sun Yaki Kabilanchi da Bangarenci Don Kawar da Matsalolinsu
Inaso Mu Nazarci Wani Abu Muhimmi Daga India, Duk Matsalar da Kukaga India tayi Film akai to Ta Shiga Matsalar ne tun tun Tuni Kuma Sun Kawar da Ita Saboda Haka Suke Nunawa Duniya Wannan Matsalar,,, to a Hakan Kuma Yayin da Suke Nunawa Duniya Matsalar da S**a Shiga a Baya a Lokacin ne kuma Wasu Kasashen ke Kallon Wannan Matsala Su Daukota Su Kawota Garesu a Matsayin Matsala Sabuwa, Da Yawa Finafinan India Suna Kowar Da Munanan Ayyuka Sannan Basa Nunawa Duniya Hanyar Bi Don Magance Matsalar
Babbar Illar da India tayiwa Duniya Shine Yadda ta Mallaki Lasisin da ya Bata Damar Film Dinta Ya Shiga Kowacce Kasa a Duniya
Tabbas Idan Bamuyi da Gaske Ba Wadannan Matsaloli Da Kullum Karuwa Suke Bazamu iya Magancesu Ba Muddin dai India na Shigo da Finafinansu, Saboda Yayin da Muka Kwaikwayi Matsala daga Film Dinsu Kafin Mu Samu Hanya da Damar Kawar da Ita Sun Sake Kawo Mana Wata Sabuwar Matsalar, Kunga Kenan ana ta Faman Tufka ne kuma ana Warwara
Sannan Rashin Ilimin Technology Yana Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Habbakuwar Matsalolinmu, Hatta Technology Se Mun Jira anzo anyi Mana, Wallahi Arzikin da Allah Ya Jibge a Kasarmu Nigeria da Muna da Ilimin Technology na Tabbata Se Mun Kere Tsara
Bincike Ya Tabbatar Mana da Cewa a Kasarmu Nigeria Babu Abun Yarwa Sedai Rashin Sanin ya Zamuyi da Abun Yasa Zakaga Muna Mutuwa akan Arziki amma da Talauci
Allah Ubangiji Ya Datar Damu Duniya da Lahira Albarkacin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam Ameen
✍ Abdulaziz Sani Fulatan