21/08/2026
Alamomin Annabtar Manzon Allah SAW.
Farkon alamar Annabtar Manzon Allah SAW da ake iya gani itace: tsaga girjinsa mai girma da akayi. An tsaga ƙirjin Manzon Allah SAW sau huɗu a rayuwar sa SAW.
1. Lokacin yana ƙaramin shekaru a wurin Halimatus Sa'adiyyah.
2. Lokacin yana shekara goma.
3. An tsaga ƙirjin sa a lokaci da Mala'ika Jibrilu ya fara zuwa masa da Wahayi.
4. A daren Isra'i da Mi'iraji kamar yadda yazo a Hadisai.
Alamar Annabta ta biyu shine: Khatamun Nubuwwa ( Hatimin Annabta) wata alama ce ko tsoka ce ta ɗago a allon kafadar sa na gefen hagu tana feshin haske da kwarjini da kamshi wanda yake nuna alamar cewa shi Annabin Allah ne SAW.
Alama ta uku itace : Al'ru'uyas Saliha wato Kyakkyawan Mafarki ko Mafarkin gaskiya. Manzon Allah SAW ya kasance yana yin mafarki kuma sai abunda ya gani a mafarkin nan yaz kamar hasken safiya, yana ganin haske kuma yanajin sauti kuma duk abunda yagani a mafarki shine ke faruwa a zahiri.
Yana daga cikin alamomin Annabtar sa: Duwatsu da bishiyoyi sunayi masa sallama kuma girgije nayi masa inuwa.
Allah ya bamu albarkacin Manzon Allah SAW.
Ya Allah ka bawa mahaifiyata lafiya dan darajar Manzon Allah SAW.