16/05/2025
Wani ɗalibi da ya samu tallafin karatu daga Ministan muhalli ya samu maki mafi yawa a JAMB a Arewacin Najeriya
Wani ɗalibi da ya ci gajiyar shirin tallafin karatu da Ministan Muhalli, Malam Balarabe Abbas Lawal ya ƙaddamar, ya fi kowa samun maki a Jarrabawar UTME ta bana a Arewacin Najeriya, inda ya samu maki 345.
Jaridar Punch ta rawaito cewa ɗalibin, mai suna Aminu Ahmad, na ajin ƙarshe a makarantar Al-Hudahuda College da ke Zariya, Jihar Kaduna.
Ahmad ya doke ɗaruruwan ɗalibai daga sassa daban-daban na Arewa don ya zama na farko a wannan jarrabawar JAMB ta bana.
Ahmad ya samu maki kamar haka: Lissafi – 96, Physics – 98, Chemistry – 94, da Turanci – 57.
Aminu na cikin jerin ɗaliban da su ka samu tallafi daga wannan shirin na musamman da Ministan ya ƙirƙira domin tallafa wa ɗalibai marasa galihu a Arewacin Najeriya, da nufin rage gibin da ke tsakanin masu hali da marasa shi a fannin ilimi.